Pulse.ng logo
Go

Shugaban kasa Dalilin da yasa Buhari ke neman zarcewa

Sanarwar ta kara da cewa shugaban ya bayyana anniyar sa ne domin hukumar zabe su san matsayin sa tun kafi zabe ya gabato

  • Published:
Buhari appoints two Deputy Directors-General for the NIA play

President Muhammadu Buhari

(AFP/File)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban dalilin da ya sanya ya sanar da kudirin sake tsayawa takara a zaben 2019 shine sakamakon koke-koken da jama'a keyi na ya nemi zarcewa.

Shugaban ya sanar da anniyar sa na neman zarcewa a taron shugabannnin jam'iyar APC da aka gudanar ranar 9 ga watan Afrilu a garin Abuja.

A wata sanarwa da  hadimin shugaban Mallam Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa shugaban ya yanke shawara zarcewa bisa bukatun jama'ar kasa.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban ya bayyana anniyar sa ne domin hukumar zabe su san matsayin sa tun kafi zabe ya gabato.

Matsayin kudirin neman zarcewa

Sai dai kudirin nasa ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, wasu da dama sunyi maraba da wannan matakin da ya dauka yayin da wasu ke ganin cewa ba zai kai labari ba.

Tun ba yau ba jama'a ke neman sanin inda matsayin shugaban yake a zabe dake gabatowa ganin yadda wasu jiga-jigai ke kokarin maye gurbin sa.

Shugaban zai fuskanci kalubale da dama ganin yadda wasu ke sukar shi kan yawan tafiye-tafiye da yake yi  zuwa kasar waje domin neman magani. Wasu na ganin cewa yana fama da rashin lafiya don haka ba zai kai labari ba.Bugu da kari, a kwanan baya shugaban ya sha suka daga tsofafin shugabanin kasa Cif Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Babangida inda suka bukace shi da yayi watsi da neman zarcewa a kan kujerar mulkin kasa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.