Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta shirya liyafa ma fitattun yan wasan Kannywood mawaka da jarumai.

Gidauniyar Aisha Buhari Foundation ta shirya taron ne domin kaddamar da sabuwar faifan waka da mawakan suka shirya mai taken "sakamakon canji".

Aisha Buhari tace wakar tana isar da sako game da irin ayyukan cigaba da gwamnatin mai gidanta, shugaba Muhammadu Buhari , keyi kuma tace muhimmin abu ne jama'a su san irin aikin da gwamnati keyi wajen tallafa ma jama'ar kasa.

A sanarwar da shugaban yadda labarai na uwargidan, Suleiman Haruna, ya fitar, Aisha Buhari ta jinjina ma jaruman masana'antar nishadi ta Kannywood bisa ga gudummawar da suke bada wa wajen wayar da kan al'umma tare da haifar da zaman lafiya.

Ta ce ya zama dole a karramar jarumai domin rawar da suke takawa wajen cigaban gwamnati baya misaltuwa.

Taron wanda aka shirya daren ranar Laraba 31 ga watan oktoba ya samu halarcin shugaban kasa tare da wasu manyan ma'aikatan fadar sa.

Mawakan da jarumai sun nishadantar da baki da wakar inda mawaka 30 suka fito gaban taron wajen kwaikwayar wakar tare da taimakon jaruman fim masu rawa da amshi.

Shahararren mawaki Abdul Amart tare da wasu mawakan Hausa suka shirya wakar 'Sakamakon canji' mai bayyana ayyukan cigaba da gwamantin buhari ta aiwatar a wa'adan sa na farko da yin mulki.