Pulse.ng logo
Go

Da dumi-dumi Daga karshe, shugaba Buhari zai tsaya takara a zaben 2019

Shugaban ya sanar da haka a taron shugabannin jam'iyar APC dake gudana a hedkwatar jam'iyar dake Abuja

  • Published:
Easter Message: Buhari urges politicians to work for peace play

President Muhammadu Buhari

(Avenue Nigeria)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki labari da jama'a suka dade suna jira kan zarcewa a kan mulkin kasa inda ya bayyana ma shugabannin jam'iyar APC cewa zai fito takara a zaben 2019.

Wannan labarin ya fito a wata sanarwa da hadimin sa Bashir Ahmad ya fitar a shafin sa na kafar sada zumunta ta twitter.

Bashir ya rubuta cewa shugaban ya amince da neman zarcewa a kujerar mulkin kasa. A bayanin da ya wallafa, za'a fitar da karin bayanai kan matakin da ya dauka nan ba da jimawa ba.

Shima gwamnan jihar Kaduna  malam Nasir El-rufai ya tabbatar da labarin inda ya nuna farin cikin sa a sakon da ya wallafa a shafin sa na twitter.

Shugaban ya sanar da haka a taron shugabannin jam'iyar APC da aka gudanar safiyar yau.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.