Gwarzon kungiyar Real Madrid , Cristiano Ronaldo, yayi bankwana da kungiyar bayan shekara tara da taka leda a kungiyar.

Fitaccen dan wasan ya koma kungiyar Juventus ta kasar Italiya ranar talata 10 ga watan Yuli.

Wannan labari ya fito bayan sanarwar da zakarun kasar Italiya suka yi na cewa zakaran turai na dawo daga cikin yan wasan tawagar ta.

Kungiyar ta siya dan wasan a kan kwantiragi na pam miliyan 88 wanda zai kai tsawon shekara hudu.