Pulse.ng logo
Go

Ci mai ban haushi Abubuwan 5 da ya faru sakamakon wasan Nijeriya da Argentina a filin krosnadar dake kasar Rasha

Muhimmin abubuwa 5 da suka faru a daren jiya sakamakon karawan super eagles da Argentina

  • Published:
7 things you need to know in markets this week and Super Eagles vs Argentina match, Data rollover play

Nigeria's Super Eagles

A daren jiya hakika yan wasan tawagar Nijeriya ta Super eagkes sun nuna bajinta da nuna ma duniya cewa ta shirya damawa a da sauran kasashen duniya a gasar cin kofin duniya na 2018.

Nijeriya ta farfado daga ci biyu har inda ta zura ma Argentina kwallo hudu a raga a wasan wanda aka tashi 4-2.

 

Inaeanacho, Idowu da Iwobi suka taimaka wajen sanya kwallaIhyen a ragar argentina bayan kwallo biyu da Banega da Aguero suka zura a ragar Akpeyi.

Yan wasan sun nuna gwanintar su a wasan wanda ya sanya yan Njeriya suka jinjina masu.

Ga abubuwa 5 da suka faru sakamakon nasarar da Super eagles tayi a kan Argentina:

1. Shugaba Buhari ya jinjina masu

Shugaban bai boye farin cikin sa bisa ga nasarar da suka samu. Ya rubuta "Ina taya tawagar super eagles da sauran yan Nijeriya murna da wannan babban nasara da suka samu a daren yau" ya rubuta a shafin sa na twitter.

 

2. Ya zura kwallo a raga wasan shi na farko da Super eagles

sabon-shiga Bryan Idowu wanda ya buga wasan shi na farko da tawagar super eagles ya samu damar zura kwallo a ragar argentina.

 

3. Dan wasan Argentina Sergio Aguero ya sume

Babban dan wasan kungiyar Manchester city ta Ingila kuma dan wasan Argentina Sergio Aguero ya sume yayin da aka je hutun rabin lokaci dakin hutawa na tawagar Argentina har ma aka wuce dashi asibiti.

 

4. Suma yan wasan sun kasa boye farin cikin su game da nasarar da suka samu.

Bayan wasan su, suma yan wasan super eagles sun bayana farin cikin su a shafukan su na kafar sada zumunta. sun yaba ma junan su game da hadin kan da suka bada tare da gwaninta da suka nuna a wasan.

 

5. suma yan kasan ba'a baro su baya ba

 

Tsokacin da yan Nijeriya suka yi na bada kwarin gwiwa wajen damawa a gasar cin kofin duniya badi yana ta yawo a duniyar gizo.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement