Jigon jamiyar mai mulki ta APC, Chris Ngige, ya baiwa dinbim magoya bayan jamiya mamaki a wajen taron yakin neman zabe da aka shirya a garin Ado Ekiti sakamakon tuntunben harshe da yayi.

Yayin da yake jawabi a taron wanda aka gudanar ranar Talata 10 ga wata, ministan yace " A dawo da Fayose" a maimakon Fayemi wanda ke neman kujerar gwamna karkashin jam'iyar sa.

Sai da tunatarwar mai jagoran taron tsohon gwamnan jihar Anambra ya gyara bakan sa.

Lamarin dai ya zamanto abun dariya ga dinbim jama'ar dake wajen taro ciki har da shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyar  APC.

Cikin gaggawa bayan ya gane kuskurensa Chris Ngige ya baiwa jama'a hakuri inda yace sunan " Fayose" ya shige masa kai domin suna kama da " Fayemi".

Bisa ga wannan tuntuben da yayi, jam'iyar adawa ta PDP ta bata sakaci ba wajen yi jigon isgili. PDP ta wallafa a shafin ta ta tuwita bidiyon inda ministan ya furta kalaman tare da rubuta cewa yana masu kamfe.

[No available link text]

A zaben jihar da za'a gudanar ranar Asabar 14 ga watan Yuli, tsohon ministan ma'adanai, Fayemi, yana neman komawa kan kujerar gwamna wa'adi na biyu bayan na farko da yayi tsakanin 2010 zuwa 2014.

Zai nemi ya maye gurbin Gwamnan yanzu, Ayodele Fayose, wanda wa'adin sa ta zo karshe bayan shugabantar jihar sau biyu.

Gabanin zaben, Dr Kayode Fayemi, ya aje aikin sa a majalisar gwamnatin kasa domin mayar da hankali wajen nemna kuri'ar jama'ar jihar Ekiti.