Pulse.ng logo
Go

Ziyara Buhari zai gana da Trump, ga abubuwan da zasu tattauna akai

Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Amurka 30 ga watan afrilu inda zai tattauna kan wasu muhimman batutuwa da shugaba Donald Trump

  • Published:
Shugaba Buhari zai gana da Donal Trump na kasar Amurka a fadar White house play

Shugaba Buhari zai gana da Donal Trump na kasar Amurka a fadar White house

(CNN)

Shugaban kasa Muhammadu yana dap da ganawa da shugaban kasar Amurka Donald Trump inda zasu tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa.

A wata takardar sanarwa da sakataren watsa labarai na fadar shugaban Amurka ta White house,  Sarah Huckabee Sanders ta sanar cewa shugaban Amurka zai gana shugaban Nijeriya ranar 30 ga watan afrilu  a fadar sa.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugabannin zasu tattauna kan batutuwa da ya hada da, hanyoyin kawo sauyi kan harkar kasuwanci da yaki da ta'adanci da kuma hanyar ingantar lamura a Nijeriya ta yadda zata cigaba da zama jagorar dimokradiya a nahiyar Afrika.

Sakataren ta kara da cewa akwai kyakywar alaka tsakanin kasar Amurka da Nijriya.

Wannan ba shi bane haduwar su na farko tunda shugaba Buhari ya hau kujerar mulki, a cikin watan Satumba na shekarar 2017 shugabannnin sun hadu a taron karrama wasu shugabannin kasashen afrika da majalisar dinkin duniya ta hada.

No, Buhari isn’t 1st African president to visit Trump at White House play

Shugaba Donald Trump tare da Shugaba Buhari tare da ministan ayyukan waje Geoffrey Onyeama

(Twitter/NGRPresident)

Ziyara zuwa kasar Ingila

Yanzu haka shugaba Buhari Buhari yana kasar Ingila inda ya kai ziyarar aiki tun ranar 9 ga watan yanzu.

Shugaban zai gana da firayin ministan Ingila Theresa May kan dangantaka dake tsakanin kasar Nijeriya da Ingila.

Shugaban zai kuma tattauna da shugaban kamfanin Dutch royal plc mista Ben van Beurden da kamfanin Shell da makamantan su kan matakin zuba jari a masana'antar mai na kasar Nijeriya.

Daga karshe shugaban zai gana da wasu jami'ai na Ingila da kuma yan Nijeriya mazaunin kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.