Pulse.ng logo
Go

Shugaban kasa Buhari yayi sabbin nade-nade, ciki har da kakakin yakin neman zaben sa

Festus Keyamo zai wakilci jihar Delta a cikin jami'an hukumar da shugaban ya nada.

  • Published: , Refreshed:
Full text of what Buhari said during Lake Chad conference play

Shugaba Muhammadu Buhari

(Presidency)

Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi sabbin nadi a hukumar Nigerian Deposit Insurance Corporation (NDIC).

Cikin Mutane shidd da shugaban ya nada har da barister Festus Keyamo wanda aka nada kwanan baya a matsayin kakakin yakin neman zaben zarcewan shugaban a zaben 2019.

Wannan labarin ya fito ne  a wata wasika da shugaban ya tura ga yan majalisa domin yardar su, wanda shugaban majalisar Bukola Saraki ya karanta a zaman da suka yi ranar talata 8 ga watan Mayu.

Ga sunayen sauran mutanen da ya nada kamar haka: Chief Olabode Akeem Mustapha daga jihar Ogun, Alhaji Garba Buba daga jihar Bauchi, Bello Garba (jihar Sokoto) Brigadier-General Joseph O.J Okalogu (jihar Enugu), Mustapha Adewale Mudashiru jihar Kwara), Mr Adewale W. Adeleke (jihar Ondo).

Bayan ga haka, shugaban ya tura sunan Ateru Garba Madami, a matsayin wanda zai maye gurbin kwamishnan hukumar zabe na jihar Niger.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.