Pulse.ng logo
Go

Shugaban kasa 'Babu hutu har sai bayan an kubutar da yan matan da aka sace'

hugaban ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara jinkai jihar Yobe ranar laraba 14 ga wata domin tattatunawa kan batun daliban makaranta da aka sace a jihar

  • Published: , Refreshed:
Shugaba  kasa ya tattauna da shugabanin jihar Yobe play

Shugaba  kasa ya tattauna da shugabanin jihar Yobe

(Instagram/buharisallau)

Shugaban kasa  Muhammadu Buhari yace gwamnatin sa baza ta huta har sai bayan an kubutar da yan matan da mayakan boko haram suka sace.

Shugaban ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara jihar Yobe ranar laraba 14 ga wata domin tattatunawa kan batun daliban makaranta da aka zasce a jihar.

Shugaban ya samu tarba daga gwamnan jihar Ibrahim Gaidam bayan haka ya tattatuna da jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya na jihar da sauran shugabannin al'umma na jihar.

play (Instagram/buharisallau)

 

Yana mai cewa "babu hutu har sai bayan an kubutar da dukannin matan yan chibok da Dapchi ga baki daya.

"Daliban yan kasa kamar sauran jama'a kuma suna da hakkin gudanar da yancin walwala wajen cinma burin su a rayuwa.

Shugaban yace hakkin su ne wajen bada kariya ga dalibai.

Ya kara da cewa gwamnatin sa ta dauki alkawarin tabbatar da tsaron a dukkanin yankunan dake kasar.

A jawabin sa yayin da ya amshi bakoncin tsohon sakataren ayyukan waje na Amurka, shugaban ya bayyana cewa a shirye suke wajen neman sulhu da Boko haram domin kubutar da yan matan.

Yau kwana 17 kenan da yan ta'addar suka far ma al'ummar dapchi dake jihar Yobe har suka yi nasarar yin awon gaba da yan matan makaranta su 110.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement