Pulse.ng logo
Go

June 12 Maimako 29 ga watan Mayu, shugaba Buhari ya sauya ranar dimokradiya

Duk a cikin takardar, shugaban ya kaddamar da ranar 12 a matsayin sabuwar ranar dimokradiya a Nijeriya kuma ranar hutu a duk fadin kasar.

  • Published:
Shugaban kasa Muhammadu Buhari play

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

(Instagram/buharisallau)

Domin karrama tsohon dan takarar shugaban kasa Alhaji Moshood Abiola shugaban kasa ya sauya ranar dimokradiya a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ya sa hannu, shugaban yace wannan mataki ya zo ne domin tunawa da zaben ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.

Ana ganin cewa a zaben wanda ake la'akari cewa shine zabe mafi sahihanci a nijeriya, Abiola ne yayi nasara lashe amma gwamnatin mulikin soja na wancan lokaci ta soke shi.

Shugaba Muhammadu Buhari yace zai karrama marigayin da lambar yabo mafi girmamawa ta GCFR a ranar Talata na mako mai zuwa yayi bikin tunawa da wannan ranar.

Duk a cikin takardar, shugaban ya kaddamar da ranar 12 a matsayin sabuwar ranar dimokradiya a Nijeriya kuma ranar hutu a duk fadin kasar.

Sai dai wannan matakin na zama ranar hutu zai fara daga shekara mai gabatowa ta 2019.

Sai dai shugaban bai bayyana ko hakan na nuna cewa an sauya ranar mika mulki ga sabuwar gwamnati wanda aka saba yi a ko wace ranar 29 ga watan Mayu bayan zabe.

Bugu da kari shugaban zai kuma karrama Ambasada Baba Gana Kingibe wanda ya tsaya a matsayin mataimakin Abiola da lambar yabo na GCON.

Baya ga haka shima babbana lauya Gani Fawehinmi wanda yayi tsayin daka wajen gani an tuna da wannan ranar zaben.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.