Pulse.ng logo
Go

Hukumar tsaro ta cikin gida Shugaba Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin shugaban DSS

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, sabon shugaban hukumar zai fara aiki ba tare da jinkiri daga ranar 14 ga watan Satumba.

  • Published:
Buhari cancels FEC meeting for on-going political activities play

President Muhammadu Buhari

(AFP/File)

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon shugaban hukumar yan sandan farar kaya.

Kakakin shugaban Garba Shehu ya sanra da labarin haka ranar alhamis 13 ga watan Satumba

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, sabon shugaban hukumar zai fara aiki ba tare da jinkiri daga ranar 14 ga watan Satumba.

Kakakin ya kara da cewa sabon shugaban hukumar cikakken jami'in hukumar ne ciki-da-waje kuma ya samu horo mai tarin yawa.

Yusuf Magaji Bichi zai maye gurbin  Mathew Seiyefa wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar mai rikon kwarya a ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya nada shi bayan da ya sallami tsohon shugaban hukumar Lawal Daura.

Sallamar shi ya biyo bayan mamayar da jami'an hukumar suka yi ma zauren majalisar tarayya inda suka hana ma'aikata da yan majalisar shiga ko fita.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement