ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaban kasa zai dawo nan ba da jimawa, inji Osinbajo

A daren jiya ne Osinbajo ya gana da shugaban kasa a birnin London inda yake jinyar rashin lafiya.

Acting President Yemi Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa ya bayyanar da wani labari sakomakon ganawar da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari inda yace “nan ba da jimawa zai dawo”.

Osinbajo ya gana da shugaban kasa a daren jiya 11 ga watan Yuli a Abuja house dake birnin London inda yake jinya.

Bayan ganawar da ta ɗauki sa’a guda, Osinbajo yace yaje ne don ganin lafiyar shugaban kasa.

Mukaddashin shugaban kasa yayi ma manemai labari bayani inda yace, “hakika tun ba yau nake magana da shugaban kasa ta hanyar waya shine na yanke shawarar zuwa ganin shi kuma in sanar da shi yanda kasar ke ciki”

ADVERTISEMENT

“Mun yi kyakkyawar tattaunawa akan abubuwa da dama kuma yana samun sauki sosai”

“Muna sa ran dawowar shi kasar nan ba da jimawa”

Shugaban kasa yana birnin London tunda ya bar nijeriya 7 ga watan Mayu na bana don yin jinyar rashin lafiya da yake fama da ita.

Kwanan baya matar shugaban kasa Aisha ta ziyarce shi kuma a kwanan nan da ta dawo ta kara haske akan dawowar shi inda ta mayar ma Shehu Sani martani kan labarin da ya fitar a kafar sadarwa na facebook ranar litinin 10 ga watan Yuli.

Uwargidan tace  “Allah ya amsa addu’o’in kananan dabbobi masu rauni, ana gab da koran karnuka da kuraye daga masarautar. Mun yarda da addu’o’in tare da goyon bayan da kananan dabbobi suke bada wa, Allah ya taimaki kananan dabbobi, Allah ya taimaki nijeriya.”

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT