ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Budurwa ta maka wani saurayi kotun shari'a dake Kaduna kan laifin kin auren ta bayan yayi mata ciki

Maryam ta sanar ma kotun cewa ita da saurayin sun kwashi kusan shekara daya suna soyayya kuma yayi mata alkawari cewa zai aure ta sai dai daga baya ya bijire bayan yayi mata ciki

Ta maka shi kotun shari'a dake nan Magajin gari dake garin Kaduna ranar laraba 21 ga watan maris.

A bisa labarin da NAN ta ruwaito, Maryam ta sanar ma kotun cewa ita da saurayin sun kwashi kusan shekara daya suna soyayya kuma yayi mata alkawarin cewa zai aure ta sai dai daga baya ya bijire bayan yayi mata ciki.

"Yayi mun alkawari cewa zai aure ni bayan na haihu amma da hakan ya faru ya kaurace ni bayan na haifar mai da jariri ya kuma bayyana mun cewa ya fasa yin auren.

Ita dai Maryam ta nemi kotu data zantar da hukunci na shi Salihu ya amince kuma ya karbi jaririn da ta haifar masa a matsayin mahaifi.

ADVERTISEMENT

Sai dai shi matashin wanda ake zargi da laifin ya karyata maganar ta inda  ya sanar cewa tun dama ba soyayya suke ba, alakar su ya saya amatsayin abokai.

"Tana yawan zuwa shago na, muna wasa da dariya wanda dalilin haka yasa muka dan shaku amma a gurina babu wata kallon da nike mata face na abokiya ta" Ya sanar ma kotun.

Ya kuma nisantar da kanshi kan alaka da jaririn da ta haifa inda yake cewa cikin da ta dauka ba nashi bane.

Mai Shari'a Malam Musa Sa'ad ya bukaci su da su gabatar da masu shaida da waliyan su gaban kotu kana ya daga ranar saurara kara zuwa ranar 26 ga watan Maris domin su samu damar bayyanar da masu shaida.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT