A bayanin da kakakin rundunar sojojin Nijeriya Birgediya Janr Texas Chukwu yayi, yace dakarun 28 task force suka gano ta ranar lahadi 29 ga watan Yuli.
Kamar yadda suka gano sunanta Zainab Mohammed kuma sojojin zasu mika ta ga hukuma bayan kammala bincike.
Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa sojojin sunyi nasarar dakile wani hari da mayakan ke shirin kaiwa kuma sun gano bindigar AK-47 tare da kunshin harsashin bindiga.