Dakaru sun daƙile ʼƴan taʼádda da suka tafi gagárumín aiki na sayén ƙwayoyi na bi da cûtar da ake kámuwa tá hányár yin jimaʼi da mai ƙarin ƙuzari
An maida kayaki kamár kartanin Viagra wanda yáke maganin taɓaɓarewan jiki.
Gidan Jarida na Premium Times sún kawo wannan rahoto.
Dakarun Najeriya waɗanda ke bataliyan na Ƙarfi mai lamba 112, sun daƙile wasu mutane da suka koƙárin tsálakáwa a kan babúr daga garin Anadawa zuwa Minari a Jihar Borno.
An samu labari cêwa sojoji sun bi sáwun waɗanda ake zargi da taʼáddanci zuwa Anadawa. Da suka gáne cêwa suna da makami, sojoji sun búɗe musu wútar bindiga.
Mun samu labari cêwa waɗanan ʼƴan taʼádda sun mutu a nán také, kuma dakaru sun dawo da bindigogi biyu da harsáshi fákiti goma sha-takwas na bindiga mai ƙarfin 7.62MM na ƙungiyar sojojin ƙasashen waje, mai suna NATO.
An káma su da takarda na jerin saye-saye wanda zasu yi. A cikin wannan takarda, sun yi lissafin magunguna da sauran abubuwa da yawa.
A cikin wannan takarda, sun rubuta kartani na Viagra, wanda áke bayarwa domin matsalar rashin ƙuzarin namiji. Sun rubuta MMC Sex Men wanda ake sha domin ƙarin ƙuzari.
A cikin jérin abubuwan da za su saye, sun rubuta kartanin shayi na Maxman Coffee da kuma shayin Viamax Power Coffee.
Duka waɗanan magunguna na ƙarin ƙuzari ne. Bugu da ƙari, suna neman su saye ƙwayoyi mai maganin kabba da ciwon sanyi, da maganin tetanus da Oxytocin- mai hanna jini zuba.
A shekara na 2015, sojojin Najeriya masu yaƙi a Arewa ta Gabas, sun kamaʼƴan Boko Haram, kuma sun kore su daga sansanoninsu. An cimma maganin ƙuzari, robar, da sauran ƙwayoyi.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng