ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ƴan taʼadda Boko Haram ɗari sun kai harin bam a sansanin masu gudun hijra wanda yake garin Rann

Ƴan Boko Haram sun kai hari a sansanin masu gudun hira a garin Rann kwana uku bayan Sojojin Sama na Najeriya sun kai musu harin bamabamai cikin bazata/kuskure.

Boko Haram

Kusan ƴan taʼadan Boko Haram guda ɗari sun ƙaddamar da hari a ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu. Sun kai harin a sansanin masu gudun hijra a garin Rann cikin Jihar Borno.

An aikata  harin bayan Sojojin Sama na Najeriya sun jefa musu bambamai cikin kuskure. Amma, Sojojin Ƙásà na Najeriya wanɗanda ke tsaron garin sun mayar da harin.

Mun samu labari daga gidan jaridan Premium Times cewa sojojin sun ɗauki saʼoi da yawa a yayin da sun yaƙan ƴan taʼadda, kafin su ci nasara bayan sun kashe takwas daga cikin makiyan. Daya daga sojojin najeriya ya ji rauni a cikin wannan rikici. Ana tunanin cewa waɗanan su ne ƴan taʼadda wanda sojojin sama suka yi niyyan kai ma hari a kwanakin da suka wuce.

Sansanin masu gudun hijra a garin Rann ya zama batun labari tun ranar Talata 19 ga watan Janairu a lokacin da an jefa bamabamai uku wanda ya hallakar da mutane fiye da 100.

ADVERTISEMENT

Sojin Sama na Najeriya sun yi kuskure da jefan bam wajen yaƙi bayan an basu labarin taron ƴan taʼadda a kewyen Rann.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT