Shugaban ƙaramin hukumar Mayo-Sava, mai suna Babila Akaou, ya yi bayáni cewa nakiya na farko ya tashi a Mora. Ɗaya daga cikin ʼƴan matan ta mutu a nán táke, kuma mutane huɗu sun ji rauni.
ʼƳan unguwa sun kashe ʼƴar uwanta kafin nakiyan da yake ɗaure da ita ya tashi. ʼƳan ɗarikar Boko Haram sun sha yin amfani da ʼƴan mata da yara wajen ta da nakiyoyi kai-akai. Waɗanan ʼƴan mata suna da shekara tsakanin 13 da 18. ʼƳan tsaró sun gani lokacin da suka shiga garin Akaou da safe a ranar kasuwa. Wani ɗan gari mai suna Abou ya ce:
"Sun kama hanyar kasuwa. Ba su sanyá takalmá ba, wannan shi yá jáwo hankalin mu zuwa wajen su."
Abou yá ce ʼƴan matan sun wuce gaban shi a daidai ƙarfe bakwai na safe.
Masu kisan kai suna kai hari a Mora wanda yake kilomita talatin daga iyakan Najeriya. Sun kai irin wannan hari cikin Kamerun kullum, amma ƙungiyar International Crisis Group sun yi rahoto a wannan wata cewa an rage hári sosai tun watan Satumba. Wannan ya sa manazarta su yi imani cewa ƴan Boko Haram sun rasa ƙarfi.