Gwamnatin tarayya ta bada ranar litinin 2 ga watan Octoba a matsayin ranar hutu.
Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da ranar litinin 2 ga watan Octoba a matsayin ranar hutu
Dambazau yayi kira ga 'yan Nijeriya da su cigaba da bunkasa zaman lafiya da hadin kai a ƙasa
An bada wannan hutun don murnar bikin cika shekaru 57 da samun yancin kai.
Bisa rahoton jaridar Vanguard, ministan harkokin cikin gida Lt.Gen Abdurahman Dambazau yayi wannan sanarwar.
A wata takada da sakatere na dindin na ma’katar Abubakar Magaji ya sa hannu, ministan yana ma 'yan Nijeriya barka na cika shekara 57 da samun yanci.
Dambazau yayi kira ga yan Nijeriya da su cigaba da bunkasa zaman lafiya da hadin kai a ƙasa.
Nijeriya ta samu yancin kai ranar 1 na watan Octoba 1960 bayan ta kwashi shekaru 59 karkashin mulkinmallakar turawan Britaniya.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng