Ministan sharia Abubakar ya aurar da diyar ranar asabar bikin auren ya samu halarcin manyan masu hannu da shunu dake kasar ciki har da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

An daura auren Zakiyya Abubakar Malami da Saifullahi Mai gishiri a fadar mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Bashar.

Jihar Kebbi ta samu bakoncin manyan baki da suka halarci bikin daurin auren.

Cikin bakin da suka halarci bikin akwai gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu tare da takwarorin sa na jihar Katsina, kaduna, Jigawa, Sokoto da Zamfara.

Shima sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya halarci bikin tare da shugaban hukumar Kwastam da na ma'aikatar shige da fice.

Wasu daga cikin ministocin kasa da suka halarci bikin sun hada da ministan tsaro, ministan sufuri, ministan ilimi da ministan mai.