Pulse.ng logo
Go

Cakwakiya a zauren majlisar tarayya Kalli bidiyon yadda yar majalisa tayi fito na fito da jami'an DSS da suke tare hanyar shiga majalisar tarayya

Jami'an sunyi ma zauren majalisar kawanya ne a safiyar yau inda suka hana ma'aikata da yan majalisar shiga harabar zauren.

  • Published:
DSS seals entrance to NASS as plot to impeach Saraki thickens play

DSS takes over NASS

(Pulse)

Yar majalisar wakilai dake wakiltan jihar Ribas Boma Goodhead tayi halin maza inda take fito-na-fito da jami'an rundunar DSS ta suka tare hanyar shiga farfajiyar majalisar dokoki.

A cikin bidiyo da majiyan mu suka turo mana, an gan inda yar majalisar take daga murya ga jami'an da suka sirrace fuskokin su tana mai cewa "Sai ku bari ana amfani daku wajen cin mutunci, kuu kashe mu idan zaku iya, mutane nawa zaku iya kashewa a nan?".

 

Jami'an sunyi ma zauren majalisar kawanya ne a safiyar yau inda suka hana ma'aikata da yan majalisar shiga harabar zauren.

Wani kwakkwarar majiya ya shaida mana cewa jami'an sun tare zauren ne duk cikin matakin tsige shugaban majalisar wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ranar 31 ga watan Yuli.

Kawanya da jami'an suka yi ya biyo bayan ganawar da wasu sanatocin APC suka yi shugaban DSS tsakar daren ranar Litinin.

Majiya ya cigaba da cewa APC ya shirin kaddamar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar tare da Sanata Hope Uzodinma a matsayin mataimakin sa matukar idan an hana masu rike da matsayin daga shiga zauren yau.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement