Pulse.ng logo
Go

Garkuwa da mutane Barayi sun sace wani bature dan kasar jamus a jihar Kano

An sace shine a hanyar shi na zuwa wajen aiki, sun kuma kashe dan sanda dake tsaran shi sakamakon harin da suka kai masa

  • Published:
German embassy yet to respond to abduction of citizen in Kano play

Illustrative photo

Wasu masu garkuwa da mutane sun sce wani bature dan kasar jamus hanyar sa na zuwa wajenn aiki.

Baturen mai suna Micheal Cremza injiniya ne a kamfanin Dantata and Sawoe ya shiga hannun masu garkuwan hanyar shi na zuwa wajen aiki. an kashe jami'in tsaro dake tsaron shi sakamakon harin da barayin suka kai masa.

Wani ganau mai suna Abubakar Muhammad ya shaida cewa masu garkuwan sun bude wuta yayin da suka far ma motar baturen kana suka kashe dan sanda dake tsaran shi. Sakamakon harbin iska da suka yi, arsashi ya samu wani direba dake wajen inda lamarin ya faru.

Rundunar yan sanda na jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin

Mai magana da yawun rundunar DSP Magaji Majia ya shaida wa manema labaraiĀ  cewa masu garkuwan sun kai ma baturen harin bazata kana sun kashe jami'in dake tsaran shi.

Kamar yanda ya sanar, lamarin ya faru a daidai hanyar sabon titin Madobi dake Kano ranar litinin 16 ga watan Afrilu.

harkar sace mutane ya fiye zama ruwan dare a Nijeriya, abun mamaki game da lamarin shine ganin yadda lamarin ke kara kumari a arewacin kasar.

Mafi yawanci ire-iren sace baure ma'aikatan manyan kamfanuka ya fiye faruwa a yankin Neja Delta.

Wannan dai ya kara nuna irin matsalar tsaro da kasar da fama da ita.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.