ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ba zan taba daina yin fashi domin na shaku da yin haka - inji ɓarawon motoci

Wani gawurtaccen barawon mota ya amsar laifin cewa ya shaku da yin sata kuma ba zai taba dainawa ba

Wani ɓarawo mai shekaru 31 kuma uban yara biyu wanda ya dauki yin sata a matsayin sana'a ya shaida ma rundunar yan sanda dake Onikan nan jihar Legas cewa ya shaku da yin sata kuma baya tunani zai taba dainawa.

Mai laifin Joshua Tabiti wanda ya shaida cewa ya kan yi aikin direban mota ya amsa laifin satar motoci kuma ya fara yin sata tun yana yaro.

Rundunar yan sanda ta musamman daga ofishin mataimakin sufeto janar reshin yankin yammacin kasar ta kaddamara da Tabiti tare da sauran abokanan aiki shi a farfajiyar su dake Legas.

Tawagar ɓarawon sun hada da Oluseye Arokoyo (mai lura da inda motoci suke) mai shekaru 34, Ahmed Alli (Asali yana aikin askin gashi) mai shekaru 24 da mai karban motocin satar  Moses Ofoke wanda ke da shekaru 31.

ADVERTISEMENT

Rahotanni ya nuna cewa hukumar yan sanda sun kama su ta hanyar bibiyar wayoyin su tare da yi masu barazanar siyan motocin da suka sace.

Wani majiya daga rundunar yan sanda yace barayin sun saci motoci uku a ranar da aka kama su kuma jami'an sun kwato motoci 26 daga hannun su tare da gano ta hanyar bin diddigi motoci 11 a jihar Ondo wanda saka satar.

Yayin da yake amsa laifin sa Tabiti ya shaida wa yan sanda cewa yayi iya bakin kokarin sa wajen daina yin sata amma bai samu nasara ba ya kara da cewa suma iyayen sa sunyi kokarin yin haka amma duk ba'a samu mafita ba.

mataimakin sufeto janar na yan sanda na yankin Adamu Ibrahim ya jinjina ma jami'an bisa gangarumin kamu da suka yi inda ma ya kara masu kwarin gwiwa wajen kawar da laifufuka a yankin.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT