ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An dakatar da wani mutum a wurin aikinsa bayan ya ci mutuncin matan Obama a shafin Tuwita

Wani mutum wanda ya zagi Michelle Obama ya jawo ma kansa matsala bayan an dakantar da shi a wurin aikinsa.

An dakatar da wani mutum a wurin aikinsa bayan ya ci mutuncin matan Obama a shafin Tuwita

Mun kawo muku labarin wani mutum mai kauɗi wanda ya ci mutuncin Michelle Obama (waton matan shugaban ƙasar Amirka wanda zai sauka cikin kwanan nan). An dakatar da shi a wurin aikinsa domin baƙin maganan da ya yi mata akan Tuwita.

A cikin rahotanni, wannan mutum ya yi ma matan Obama baƙin magana game da hoton da ta yi da karnuka a ranar bikin haihuwa wanda aka yi. Ya yi mata jifaʼi a shafinsa na Tuwita haka:

"Saran ki suna rungume da ƴaʼƴansu maza, amma kina rungume da karnuka"

Wannan kalaman da ya yi ya jawo muhawara akan yanan gizo. Mutane da yawa, har dai mata, ba su karɓi wannan magana cikin sauƙi. Sun kai masa hari sossai domin nuna banbanci tsakanin ƴaʼƴa na maza da mata. Sun ce ya yi waɗanan kalamai domin rage darrajan ƴan mata, ganin cewa Michelle bata da ɗa (namiji), sai ƴan mata biyu kawai. Michelle Obama ta yi gaisuwa akan shafinta haka:

ADVERTISEMENT

"Ina yi muku godiya domin gaisuwan da kun yi mini. Ina godiya domin damar da kun bani na bautan ƙasar Amirka a matsayin Shugaban Mata.

Bayan ya karanta wannan rubutu akan shafin Michelle Obama, ɗan Najeriya wanda ya zage ta ya bayar da amsa haka:

"Saran ki ƴan mata suna rungume da ƴaʼƴansu na maza, amma kina rungume da karnuka. Sannu.

Yawancin mutanen da ke muhawara da ni suna fama da irin wannan damuwa domin ana baƙin ciki da su saboda rashin haihuwan ɗá. Munafikai! Bayaninku bai da muhimmanci. Na tsaya akan Gaskiya.

A nahiyar Afirka, idan macce ba ta haifi ɗa ba, girman ta zai faɗi!!! Wannan bayani mai ɗaci ne, amma gaskiya ne.”

ADVERTISEMENT

Bayan wannan rubutu ya zagaya yanan-gizo da sauri, kamfanin da yake aiki sun dakantar da mutumin har tsawon mako uku. Ko da yake ya rubutu wasiƙar na uzuri da hakuri, an ba shi wasikar.

Duk da wannan lamarin da ya same shi, mutumin ya sake yin kuka akan Tuwita game da abubuwan da ya same shi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT