Pulse.ng logo
Go

Ziyarar shugaban kasa Babu tabbas ko shugaba Buhari zai dawo kasa bayan kwanaki hudu - inji kakakin sa

Mataimakin shugaban kan harkokin watsa labarai, Femi Adeshina ya shaida cewa hakika komai na Allah kuma babu tabbas ko shugaban zai wuce kwananki da aka kayyade

  • Published:
Shugaba Muhammadu Buhari play

Shugaba Muhammadu Buhari

(Nigerian tribune)

Fadar shugaban kasa tayi fashin baki kan ziyarar ganin likita da shugaban Buhari zai yi zuwa kasar Ingila wanda zai dauki tsawon kiwanaki hudu.

Mataimakin shugaban kan harkokin watsa labarai, Femi Adeshina ya shaida cewa hakika komai na Allah kuma babu tabbas ko shugaban zai wuce kwananki da aka kayyade masa.

Ya bayyana hakan ne tatin da ya zanta da gidan telebijin Channels, ya kara da cewa tafiyar shugaban ba wanda zata tada hawan jini bane domin yaje duba lafiyar sa ne ba jinya zai je yi.

Yayin da aka tambaye shi ko shugaban zai wuce kwanaki hudu da aka sanar cewa zai yi , ganin yadda ya wuce ranakun da aka kayyade masa a tafiyar da yayi a baya, Femi Adeshina yana mai cewa Allah kadai ne masani dangane da haka.

Sai dai ya kara da cewa, idan komai ya tafi yadda ya kamata, shugaban zai dawo kasar ranar asabar mai gabatowa.

Ya jaddada cewa, ba lalle bane shugaban ya bayyanar da labarin lafiyar sa ga jama'a domin yana da yancin boye sirri lafiyar shi.

Ziyarar ganin likita

Shugaban zai kai ziyarar ganin likita zuwa kasar Ingila na kwanan hudu. zai dawo ranar 13 ga wata.

Kamar yadda fadar sa ta sanar, Shugaban zai kai ziyarar ne bisa bukatar likitar sa.

A sanarwar da hadimin sa Garba Shehu, ya fitar, jagoran yan Nijeriya zai koma ne bayan takaitacen haduwa da yayi da likitan yayin da jirgin dake dauke dashi ta yada zango Ingila yayin da take dawowa daga kasar Amurka.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.