Tsohon Gwamna na Jihar Niger, Muʼazu Babangida Aliyu, ya ce namiji yake aikin Kicin a gida.
Tsohon Gwamnan Jihar Niger ya ce hakiƙa namiji yake aikin Kicin
Aliyu ya ƙara faɗi cewa matsayin mata shine zaman ɗaki yayin da namiji yana biyan buƙatan gida.
Aliyu ya ce ya kamata mátá su zauna a matsayin kula da ɗaki yayin da mazajensu na aikin biyan buƙata. Tsohon Gwamna ya yi wannan magana a lokacin da yake ba da lacca a babban birnin Minna. An kawo rahotonsa a jaridan Vanguard kamar haka:
"Idan muka duba wannan batun sossai a sharuddan muslunci, namiji ne yake da aikin kula da kicin yadda aka rubuta cikin Al-Quran".
"Ya kamata mace tá kula da harkan ɗaki kawai, kuma namiji zai biyar duka buƙatan matansa. Namiji yake da alhakin sayyaya daga kasuwa domin amfanin iyalinsa."
"Ga ƙaʼidan muslunci, bai kamata mace ta fita ba tare da laʼakari ba. Ya kamata sun zauna gida domin kula da yara da sauran iyali".
Ana tsamanin cêwa wannan bayani na Aliyu, ya taso domin ƙarin haske ga bayani wanda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi game da matsayin mata a kicin. Buhari ya yi wannan bayani a Ƙasar Jamus, bayan hiran matansa akan BBC.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng