Yan takarar APC a jihar Zamfara sunyi ba uwa ba riba inda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta hana jamiyar fitar da yan takara da zasu fafata a zaben 2019.

Hakan ya biyo bayan uwar jam'iyar na kasa da kuma ta jihar suka gaza cinma matsaya game da zaben fidda gwani na jihar domin tantance yan takara.

Rikici ya barke tsakanin yan takarar APC a jihar inda tawagar gwamnan jihar da daya daga cikin yan takarar gwamna, Sanata Kabir Marafa, suka samu rashin jituwa.

APC na jihar Zamafara sun samu baraka ne yayin da gwamna Abdul'aziz Yari ya nemi dan takarar da ya fitar ya zama wanda zai zama dan takarar APC na kujerar gwamna amma sauran yan takarar jam'iyar basu amince da hakan ba.

Sau da dama aka soke zaben fidda gwani ta kwamitin zabe da uwar jam'iyar ta tura jihar domin gabatar da zaben fitar da gwanaye.

Takaddamar jam'iyar a jihar ya kai ga matakin rushe shugabanin APC na jihar.

Hukumar zabe ta dauki wannan mataki na sauke yan takarar APC na jihar duba da goyon bayan kundin tsarin dokar zabe.

A cikin wani sako da kakakin hukumar, Okechukwu Ndeche, ya fitar  ma jam'iya mai mulki, hukumar tayi duba da sashi 87 da 31 na kundin zabe wajen daukar wannan matakin.

Bisa ga wannan, INEC tace jam'iyar APC bata da dan takarar gwamna da kuma yan takarar majalisun tarayya da kuma na jiha daga jihar Zamfara.