Dan takarar shugaban kasa karkashin jamiyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar a jiya lahadi 25 ga watan Nuwamba yayi bikin nadin sarautar "| wazirin Adamawa wanda masarautar Adamawa ta nada shi.

Bayan hakan tsohon mataimakin shugaban kasa ya kuma yi murnar cikar shi shekara 72 a duniya duk a rana guda.

A jawabin sa Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammad Barkindo, ya bayyana cewa an nada Atiku sarautar ne bisa gudunmawar da yake bayarwa a kasar musamman a jihar sa a bangaroriu daban-daban.

Yayi kira ga sabon Wazirin da ya tafi da sauran jama'ar jihar tare da hada kan al'ummar wajen tabbatar da cigaba.

Bikin nadin sarautar wanda aka yi a jihar mahaifar sa ya samu halartar manyan yuan siyasa ciki har da tsofaffin shugabannin kasa Cif olusegun Obasanjo tare da Goodluck Jonathan.

Sauran baki da suka halarci bikin sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara. Bayan haka tsafaffin gwamnonin Kano, Sokoto da Niger sun halarci taron bikin.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na twitter, Atiku ya nuna farin cikin sa bisa muhimmancin wannan ranar a rayuwar shi inda yayi bikin nadin sarauta da na murnar zagayowar ranar haihuwar shi.

Ya kuma mika godiyan sa ga dinbim jama'a na kusa da nesa da suka samu damar zuwa wajen taron bikin.

Atiku Abubakar shine na bakwi wanda zai rike sarautar Wazirin Adamawa,