Yace idan har ya samu damar zama shugaban kasa zai fitar da mataki na yakar ta'adanci da tsaron jama da dukiyoyin su tare da hanyoyin bunkasa zaman lafiya a yankin.

Atiku Abubakar [Twitter/@atiku]
Atiku Abubakar [Twitter/@atiku]

Atiku ya kara da cewa zai samad da hanyar gyara cibiyoyin mara sa galihu da yan gudun hijira tare da magance matsaloli da barnar ta'adanci ta haifar.

Ya fadi hakan ne yayin da ya jirgin yakin neman zaben sa ta ziyarci jihar Borno ranar Laraba.

Dan takarar ya kara da cewa yana daga cikin tsarin PDP bunkasa harkar Noma, ilimi tare da samad da ayyukan yi ga matasa.

Yayi kira ga jami'an tsaro da hukumar zabe ta INEC da su tabbatar an gudanar da zabe nagari dai dai da yadda aka tsara.

Ya kuma yin kira ga jama'a da suka zabi PDP da yan takarar ta na ko wani kujera domin jam'iyar ta samu nasara a zaben gobe.

Taron ya samu halarcin dubunan yan goyon bayan jam'iyar ciki har da dan takarar gwamna na jam'iyar a jihar Alhaji Muhammad Imam da shugaban PDP na jihar Alhaji Zannan Gaddama tare da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyar da sauran yan takara.