Pulse.ng logo
Go

Peter Obi shine abokin takarar Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa da tsohon gwamnan jiha dake kudancin Najeriya sune zasu wakilci PDP a takarar shugaban kasa na zaben 2019.

  • Published:
Atiku picks Peter Obi as running mate for 2019 election play Atiku ya gana da Peter Obi a gidansa dake nan Abuja ranar juma'a 12 ga watan Oktoba

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar PDP, Atiku Abubakar, ya zabi tsohon gwamnan jihar Anambra a matsayin abokin takarar sa na zaben 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasa da tsohon gwamnan jiha dake kudancin Najeriya sune zasu wakilci PDP a takarar shugaban kasa na zaben 2019.

A halin yanzu jiga-jigan suna cikin ganawa ta sirri a nan garin Abuja. Wani shaida dake wajen ganawar tasu ya shaida ma Pulse cewa Peter shine wanda zai mara ma Atiku baya.

Muna sa ran cewa za'a fitar da sanarwa game da zabin nan bada dadewa ba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement