Yace tun bayan Abubakar Tafawa Balewa, yankin bata kara samun damar samun shugaban kasa.

Atiku ya samu kyakkyawar tarba yayin da ya ziyarci jihar Enugu
Atiku ya samu kyakkyawar tarba yayin da ya ziyarci jihar Enugu

Dan takarar jam'iyar PDP ya bayyana hakan ne yayin da jirgin yakin neman zaben shi ya ziyarci jihar Yobe .

Atiku ya tabbatar da cewa gwamnatin sa zata baiwa mata da matasa damar yin aiki tare dashi.

Dan takarar yace idan ya samu nasara a zaben, zai tabbatar da tsaro tare da zamada da ayyukan cigaba a jihar.

Daga karshe yayi kira ga jami'an tsaro da hukumar zabe na kasa INEC da su tabbatar da sunyi aikin su yadda ya kamata ba tare da fifita wani dan takara fiye da sauran.