Bayan samun nasarar zama gwanin jamiyar PDP a zaben fidda gwani da aka gudanar garin fatakwal kwanan baya, Atiku Abubakar ya fara zawarcin abokin tsayawar takarar sa.

Zabar wanda zai mara masa baya babban aiki ne wanda zai taimaka wajen ganin cewa ya samu kuri'u da dama daga al'ummar kasar.

Sai dai kamar yadda wani kwakkwarar majiya kuma jigo a jam'iyar PDP ya shaida mana, wanda zai mara ma Atiku baya zai fito daga yankin kudu ko yankin kudu maso yamma ko kuma yankin kudu maso kudu.

Har ila yau dai majiyar ya sanar cewa suna tantance wanda jam'iyar zata zaba kuma zata zabi nagartacce kuma wanda ya cancanta duba da ayyukan alheri da yayi a bangarori da mukamai da yayi aiki.

Kai ga yanzu ga manyan mutane biyar da ake san ran cewa daya daga cikin su zai haye wajen zama abokin tsayawar takarar Atiku Abubakar a zaben 2019 kamar haka;

Akinwunmi Adesina

Tsohon ministan noma karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yana daya daga cikin wadanda PDP zata tsayar a matsayin mataimakin dan takarar ta.

Adesina ya takarawar gani wajen bunkasa harkar noma a kasa sanda yake rike da mukamin minista. Haka zalika shine shugaban bankin cigaban Afrika (AFDB) a halin yanzu.

Peter Obi

Shima tsohon gwamnan jihar Anambra ya shiga sahun wadanda jam'iyar zata tsaida daga yankin kudancin Nijeriya.

Majiyoyi da dama sun shaida cewa dangantakar shi da Atiku Abubakar ya karu kwana-kwanan nan kuma shine kan gaba wajen cike gurbin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyar PDP gabanin zaben badi.

Ngozi Okonjo Iweala

Tsohuwar ministan kudi da kasuwanci ita kadai ce mace cikin jerin wadanda ake ganin cewa zasu mara ma Atikuy baya.

Ngozi ta kware sosai a fannin kasuwanci da kudi kuma ta rike manyan mukamai a babban bankin duniya.

Bisa ga kwarewar ta a fannin kudi da kasuwanci Misis Ngozi ta kawo cigaba a fannin a Nijeriya sanda take rike da matsayin minista. Ta kuma kawo kyakkyawar alaka tsakanin gwamnatin kasar da babban bankin duniya da kuma asusun lamuni na duniya wato IMF.

A kwanan baya babban kamfanin sadarwa ta Twitter ta kaddamar da ita a matsayin daya daga cikin jagororin kamfanin masu kula da lamuran ta.

Gbenga Daniel

Shima tsohon gwamnan jihar Ogun wanda yayi mulki har wa'adi biyu yana daga cikin wadanda ake ganin jam'iya zata zaba.

Mai shekaru 62 ya kawo cigaba a fannin kasuwanci sanda yake gwamnan jihar dake yankin kudu maso yamma.

Shine shugaban cibiyar yakin neman zaben Atiku kuma ya taka rawar gani wajen tabbatar da cewa ya'yan jam'iyar PDP sun zabi gwanin a zaben da aka gudanar.

Okezie Ikpeiazu

Shima gwamnan jihar Abia na yanzu yana daga cikin wadanda ake kyautata zaton zasu mara ma Atiku baya.

Gwamnan wanda ake ma lakabi da 'shalelen' yankin kudu maso gabas shine na uku daga yankin da ake san ran cewa Atiku zai zaba.

Daga karshe majiyar mu ya sanar cewa abokin tsayawar takarar Atiku zai fito bayan shawara da nazari daga jiga-jigan PDP domin kauce ma rikici a jam'iyar.