ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

PDP tayi wa Atiku kashedi game da taron koli da zata yi

Shugaban kwamiti kuma gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa yace tawagar sa na neman tabbatar da anyi taron cikin lumana.

Ban da shi Atiku kwamitin ta kara jan kunnen sauran yan takara dake neman kujerara takarar shugaban kasa karkakashin jam'iyar.

Shugaban kwamiti kuma gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa yace tawagar sa na neman tabbatar da anyi taron cikin lumana.

Yana mai cewa "Ya zama dole muyi wannan sanarwa ga duk yan jam'iyar da wadanda suke ma jam'yar fatan alheri cewa wannan taron koli za'a yi shi ne ga ragaman yan jam'iyar kuma muna sa ran halartan mutum kasa da 3000. kuma kwamitin dake tantancewa tariga ta tantance ainihin wadanda zasu halarci taron.

"Duk wani dan jam'iya da ya ziyarci Abuja baiyi laifi ba amma ba zai samu damar shiga eagle square inda za'a gabatar da taro ba indai baya cikin wadanda kwamiti ya tantance. Munyi hakan ne domin tabbatar da an yi taron cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

ADVERTISEMENT

"Mun dauki wannan mataki ne domin rage yawan mutane a wajen taro. Ina kira ga duk wani dake neman takara da su kaurace yin kamfe a wajen taron kuma muna sa ran cewa duk wani yakin neman zabe zai tsaya ranar juma'a.

"Ba na san ran ganin yan takara musamman masu neman kujerar shugaban kasa da su kawo takardar kamfe ko kuma masu yi masu kamfe a wajen taron domin baza mu lamunta da yin haka ba.

Ga Duk wani mai neman kuri'a na zaben nan gaba musamman na takkarar shugaban  kasa, wannan taron ba wajen yin kamfe bane kuma wajen bayyana anniyar fitowa takara bane.

Ina mai tabbatarwa cewa akwai taro tra musamman wanda za'ayi dmin yin haka. Da wannan nake kira gare su da taimaka mana  a matsayin mu na kwamitin wajen aiwatar da aikin mu."

Komawar Atiku ga jam'iyar PDP

ADVERTISEMENT

Atiku yayi murabus daga jam'iyar APC ranar juma'a 24 ga watan nuwamba.

Ranar lahadi 3 ga watan disemba ne tsohon mataimakon shugaban kasa Atiku Abubakar ya sauya sheka zuwa jam'iyar da ta sanya ya zama mataimakin shugaban kasa na tsawon shekara takwas.

A cikin wani bidiyo da ya fitar kai tsaye a duniyar gizo tsohon jigon jam'iyar APC yace ya fice daga jam'iyar ne domin ta kasa cinma burin da ake zaton zata samad.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT