Wani masoyin namomin daji ya gamu da ajalin sa yayin da yake kokarin daukar hoton giwa a gandun daji na Yankari dake jihar Bauchi.

Mamacin, Abubakar, mai shekaru 45 ya kasa boye mamakin sa bayan hada ido da namun dajin sai dai a garin nuna farin cikin sa daya daga cikin dabbar ya taka shi wanda yayi sanadin mutuwar sa.

Kamar yadda labari ya bayyana bayan faruwar lamarin, dabbobin sun shige daji.

Bayan ga haka wani yaro mai shakaru 9 ya rasa rayuwar shi yayin da shiga tawagar yan kallo daga kauyen Bajama domin kallon dabbobin.

Yaron mai suna Fa'izu Ciroma Musa ya mutu ne sakamakon faduwa da yayi yayin da dabbobin suka doshi hanyar masu kallon.

Mai'aikatar gandun dajin Yankari ta tabbatar da mutuwa su biyu ranar alhamis 12 ga watan Yuli.

A cikin wata takardar sanarwa da shugaban gandun, Habu Mamman, ya fitar, mai'aikatar tace dabbobin sun fita daga inda ake tsaron su da sassafe inda suka nufi hanyar kauyen Bajama. Sakamakon kewaya da jama'ar gari suka yi ganin su dabbobin suka firgita wanda shi yayi silar faruwar mummunar lamarin.

Suleiman ya kara da cewa da jami'an ma'aikatar dabbobin suka koma shingen da aka kebe masu a gandun dajin.

Daga karshe yace bisa rashin sani da jama'ar kauyen suka bayyana wajen nuna farin cikin su ta hanyar tunkarar dabbobin da niyar yin hoto ko taba su ya haifar da rashin da aka samu.

Wasu daga cikin yan garin da lamarin ya faru sun bayyana cewa rashin sanin jama'ar garin ya haifar da rashin da suka samu. Suna cewa an raina su ne.

Habu Mamman ya bayyana cewa ma'aikatan gandun Yankari sun kai ziyarar ta'aziya ga iyalen wadanda suka rasa rayukan su.

Ya kara da cewa wannan shine karo na farko da za'a samu mummunar artabo tsakanin jama'ar garin da dabbobin gandun dajin.