ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Fim wanda Ali Nuhu bai taba irin ta ba ta lashe kyauta a bikin bana

Shirin Mansoor wanda jarumin ya shirya tayi zarra wajen zama shiri mafi kayatarwa a rukunin wasan gargajiya na harshen hausa.

Gasar African Magic Viewers Choice Awards wanda aka shirya a birnin Legas ranar asabar 1 ga watan Satumba, shirin MANSOOR ya lashe kyautar shiri mafi kayatarwa.

Shirin ta lashe kyautar sabanin sauran fina-finai da aka hada su takarar na daga cikin fitattun shirye-shirye na rukunin hausa.

A jawabin sa yayin da ya amshi kyautar Ali Nuhu ya mika godiyan sa jaruman mda ma'aikatan da suka taka rawar ganin  wajen shirya shirin MANSOOR.

ADVERTISEMENT

Hirar shi da wakilin BBC hausa jarumin yace "Ina ganin Mansoor ya samu wannan nasara ce saboda bamu taba shirya fim wanda aka yi amfani da fasahar kirkire-kirkire kamar sa ba; mun kashe kudi sosai sannan mun yi amfani da na'urori na zamani wurin daukar fim din."

Shirin wanda ke isar da darasi akan yadda mutum zai gudanar da rayuwar sa ba tare da tsangwama ba domin bai san irin jarabtar da Allah ya shirya masa.

Sabbin fuskoki Maryma Yahaya da Umar M.Shereef suka fito a matsayin jaruman shirin.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT