ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

APC zata cigaba da mulkin Nijeriya har abada inji minista

Tsohuwar yar takarar kujerar gwamnan jihar Taraba ta sanar cewa zata sake fitowa takarar gwamna a zaben 2019.

Ta furta kalaman ne a taron kaddamar da sabbin shugabannin jam'iyar APC daga jihohi 35 a garin Abuja ranar litinin 4 ga watan Mayu.

A cewarta rikicin da am’iyyar ke fama da ita a halin da ake ciki ba wani sabon abu bane a harkar siyasa. Ta kara da cewa daga lokacin da jam’iyyar ta gudanar da zaben shugabanninta na kasa babu shakka zata iya tunkarar kowace jam’iyyar siyasa a 2019.

Tsohuwar yar takarar kujerar gwamnan jihar Taraba ta bayyana cewa zata sake fitowa takarar gwamna a zaben 2019.

Tayi ikirari cewa sanin kowa ne cewa ita ta ci zaben 2015 kanan ta jaddada cewa idan akwai rai da lafiya jam'iyar APC zata lashe zabukan jihohi kamar Taraba da PDP ke mulka.

ADVERTISEMENT

Aisha wacce ta bayyana cewa Atiku Abubakara ne ubangidan ta bata nuna alama ko zata bi har jam'iyar da ya koma.

Ministan ayyuka mata ta musanta labari dake yaduwa na cewa zata sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP inda ubangidanta Atiku Abubakar yake.

Hirar ta da jaridar Premium times cikin watan Janairu ministan tace zata cigaba da zama a cikin jam'iyar APC duk da cewa a kwanan baya ta sanar cewa zata mara ma tsohon mataimakin shugaban kasa baya idan har zai tsaya takara a zaben 2019.

Tana mai cewa "Siyasa ra'ayi ne kuma babu wanda ya tilasta mun wajen sauya sheka daga PDP zuwa APC a baya hakazalika babu wanda zai tilasta mun wajen barin jam'iyar. Zan cigaba da aiki karkashin APC kuma don wannan kokarin nayi tafiya zuwa jihar Taraba domin mara ma dan takarar jam'iyar baya.

"Na san akwai mutane da dama na son ganin na bar APC amma ina mai tabbatar masu cewa ina nan cikin jam'iyar babu ja da baya. Ta yaya zan tarwatsa ginin da muka yi kokari wajen ginawa tare?, cewar Aisha Alhassan.

ADVERTISEMENT

Dangane da takarar ta, tace ta mika lamarin ga Allah domin shine wanda ke bada mulki ga wanda ya so.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT