Wasu dalibai sun nuna adawar su kan mataki mai tsauri da aka kafa domin hana satar amsa a jarabawa.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, mummunar lamarin ya faru a makarantun kwana bakwai na kasar Kenya duk a cikin shirin nuna adawa ga matakin wanda zai fara aiki nan da wata uku.

Babbar ministan ilimi na kasar, Amina Muhammed, ta bayyana hakan yayin da ta zanta da manema labarai.

Bayan ga haka, a cikin wata takardar sanar da ta fitar, ma'aikatar ilimi ta kasar ta bayyana cewa yan sanda sun kara kaimi wajen kawo karshen lamarin kuma sun kama dalibai 125.

Bugu da kari, bayan da aka gurfanar da wasu a gabanta, kotu ta kama wasu guda uku da laifi.

An kuma bayar da belin wasu dalibai biyar da ake zargi da kona makarantar sakandare ta maza ta Chulaimbo da ke Kisumu.

Daga karshe dai, sanarwar ta bukaci makarantu da su karfafa tsaro a makarantun kwana a duk lokacin da dalibai suka je cin abincin dare ko yin karatun dare.