ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Anyi musayar wuta tsakanin sojoji da yan ta'adda

A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce sojojinta sun kashe yan Boko Haram da dama amma kuma an kashe wasu daga cikin sojojin a musayar wutar da suka yi da mayakan.

Mayakan sun kai ma sojojin harin kwanton bauna a Babban gida dake nan jihar Yobe ranar Asabar 21 ga wata.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Birgediya janar Texas Chukwu ya aika wa manema labarai ta ce mayakan sun yi wa sojin kwanton bauna ne bayan sun shigo Babban gida domin neman abinci.

Kakakin  yace duk da an kashe jami'anta amma ta ci karfin mayakan na Boko Haram kuma yanzu kura ta lafa.

ADVERTISEMENT

Sai dai bai bayyana adadin sojin da suka mutu sakamakon musayar da suka yi da mayakan.

Harin dai ya biyi bayan wanda yan ta'addar suka kai kasar Chadi a garin dake kusa da iyaka da Nijeriya.

Rahotani sun ruwaito cewa akalla mutum 18 suka rasu sakamakon harin da suka kai garin.

Mayakan sunyi ma mutane da dama yankan rago tare da yin awon gaba da mata 10 a nan kudancin jihar Daboua na kasar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT