Jim kadan bayan saukar sa filin jirgi na Nnamdi Azikiwe daga jirgin sama mallakar kansa, jamian tsaro na filin jirgi  sunyi ma Atiku Abubakar, binciken kwa-kwaf.

Dan takarar shugaban kasa PDP na zaben 2019 ya sanar da labarin haka a shafin sa na Twitter inda ya bayyana cewa an tozarta shi.

Lamarin dai ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta. Jam'iyar PDP tare da sauran magoya bayan ta sun soki lamarin. Suna zargin gwamnati da gudanar da binciken domin tozarta dan takarar su.

PDP ta zargi shugaba Muhammadu Buhari da bada umarni na yin haka ga dan takarar ta.

A sakon da ta wallafa a shafin ta na Twitter, PDP ta kuma zargi gwamnatin APC da tozarta dan takarar ta duba da yadda ya fara samun farin jini a kasar.

Sai dai fadar shugaban kasa da karyata zargin da PDP tayi.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa binciken da aka yi ma Atiku ba sabon abu bane kuma jami'an sunyi hakan ne bisa yadda  aikin su ya tanadar.

A cikin sanarwar da ya fitar gane da lamarin Atiku, Hadi Sirika, ya kara da cewa jami'an sunyi binciken ne tare da mutunta Atiku.

A bayanin sa, ministan yace ka'ida ne a filin jirgi na jami'an tsaro su tunkari jirgi da ya sauka daga kasar waje domin yin bincike ko da jirgin ba na jama'a bane.

Yace shugaban kasa kadai ne ba'a bincika amma sauran ma'aikatan fadar sa basu tsira ba.