ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kotu ta tura shugaban karamar hukuma gidan yari kan zargin jefa Al-kur'ani bandaki

Wadanda ake zargi sun musanta laifin yayin da aka karanta masu laifufukan su a gaban alkalin.

Wata kotun shari'ar musulunci dake gudanar da zamanta a garin Gusau ta tura shugaban karamar Hukumar Gusau Hon. Ibrahim Tanko gidan yari.

A Rahoton da jaridar Rariya ta fitar, zai ziyarci gidan kaso  tare da kansilan hukumar mai wakiltar mazabar sabon gari Hon. Ashiru Musa Nagari tare da shugaban jam'iyar APC na mazabar sabon garin Gusau Mainasara Yahaya.

A zaman da kotu tayi an zargi su da sa hannun wajen jefa al'kurani mai girma a bandaki.

Mai shari'ar Muhammad ST, Shinkafi ya bada damar a cigaba da rikon su a gidan kaso har sai bayan kotu ta nemi  shawarar gwamnatin jihar Zamfara kan laifin su.

ADVERTISEMENT

An daga ranar saurarar hukunci zuwa 26 ga watan febreru 2018.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT