Pulse.ng logo
Go

Majalia da yan sanda Cacar baki tsakanin majalisa da babban sufeton yan sanda

Sau uku kenan majalisar ke gayatar babban sufeton domin ya bayyana gaban ta don bada amsar tambayoyin matsalolin tsaro da ake fama da ita a kasar.

  • Published: , Refreshed:

Majalisar tarayya ta nuna facin rai ga sufeton yan  sanda Ibrahim Idris, wanda ya ki mutunta goron gayatar da suka yi mashi.

Sau uku kenan majalisar ke gayatar babban sufeton domin ya bayyana gaban ta don bada amsar tambayoyin matsalolin tsaro da ake fama da ita a kasar. Bayan ga haka, majalisar zata nemi karin haske daga gare shi kan abokin aikin su, Dino Melaye wanda ke fuskantar tuhuma a hannun hukumar yan sanda.

Police dismiss officer who killed NYSC member in Abuja play

The police commissioner also said the accused policeman is currently on remand awaiting commencement of trial.

(The Nation)

 

Shi dai jagoran yan sanda ya ki amincewa da gayatar a duk lokutan da suka gayyace shi.

Dangane da jayayya dake faruwa tsakanin su, majalisar ta kira sufeton a matsayin makiyin tsarin dimokradiya

Bayan ganawa da yayi da jiga-jigan majalisar kan batun ranar laraba 9 ga watan Mayu, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya kalubalanci Ibrahim Idris bisa bijirewa da yayi wa gayyatar majalisar.

Yace babban sufeton bai cancanci rike wani mukami na jagorantar mutane a ciki da wajen kasar.

Martanin babban sufeton yan sanda

Kan batun gayyatar, shima sufeton yan sanda ya mayar da martani ga majalisar dattawa game da kalaman shugaban ta na cewa bai cancanci rike mukami a kasar ba.

Ibrahim Idris yayi karin haske kan rashin kin amince da gayyatar da aka yi masa, yace yan majalisar na neman ci masa fuska domin canza alkiblar sa wajen tabbatar da shari'a.

Yace gayatar manufa ce na ci masa fuska tare da bata masa suna kan tagomashi dake tsakanin yan sanda da sanata Dino Melaye.

Shi dai sufeton ya kara da cewa ba zai amince da gayyatar majalisa ba tare da bada dalilin sa na yin haka a kundin tsarin mulki na kasa tare da kundin hukumar yan sanda.

Bisa ga misalai da dalilan da ya bada, doka ta bashi dama na tura wakilai a taruruka da aka gayyace shi.

Kamar yadda kakakin hukumar yan sanda, Jimoh Moshood, ya sanar, bisa ga wannan dalilin sufeton ya tura wasu jami'an hukumar da su wakilce shi a kan gayyatar da majalisar ta tura. Sai dai majalisar bata amince da ya turo wasu domin su wakilce shi ba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.