Cikin yunkurin da gwamnatin yanzu keyi na yakar yada labarin kanzon kurege, rundunar yan sanda jihar Kano ta kama wani mai kula da shafin manhajar dake aikar da sako ta Whatsapp.

A labarin da BBC ta fitar, kakakin rundunar yan sanda na jihar Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar haka.

Kakakin yace rundunar ta kama su ne bayan da matar da ake ma kage ta shigar da kara ofishin su bayan da hoton ta ya fara yaduwa.

Matar wacce take ma'aikaciyar gwamnati ce tace ana yunkurin jefa rayuwar ta cikin hatsari yayin da ta shigar da korafin yaduwar hotonta a Whatsapp da nufin bata sunan ta.

Majiya yace bayan binciken da rundunar tayi suka kama mutum ukun, namiji daya da mata biyu dukanin su suna da aure.

Mutanen da aka kama dai sun shaida wa 'yan sanda cewa ba su san matar ba, kuma ba su yi yunkurin tantance labarin ba gabanin su fara yada shi, don haka sun nemi ayi masu afuwa.

An bayar da belin su daga baya