ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An saki sanata wanda aka zargi da jagorantar yan daba wajen sace sandar majalisa

Yan daba suka shiga zauren majalisar dattawa ta barauniyar hanya yayin da yan majalisa ke gudanar da zama, har suka yi awon gaba da sandar majalisa

Dan majalisar wanda ke wakiltar yankin jihar Delta ta tsakiya ya nisantar da kansa da lamarin da ya faru a harabar majalisa.

A labari da muka fitar, ranar laraba ne wasu yan daba suka shiga zauren majalisar dattawa ta barauniyar hanya yayin da yan majalisa ke gudanar da zama, har suka yi awon gaba da sandar majalisa.

Sakamakon hargitsi da tashin hankali da ya faru a zauren, jami'an hukumar yan sanda sun kama sanata Omo-agege wanda aka zargi da jagorantar yan dabar.

A cikin wata sakon sanarwa da Lucky Ajokperniovo ya fitara madadin sanatan, ya sanar cewa jami'an tsaro sun saki dan majalisar.

ADVERTISEMENT

Yace Omo-agege bai da wata dangantaka da sace sandar majalisa, inda ma ya kara da cewa dan majalisar ya garzaya zauren ne don cigaba da aikin shi.

A cewar shi, sanatan ya kora ma rundunar yan sanda bayanai dalla-dalla kan dalilin zuwan sa majalisa.

Sakamakon hargitsin da ya faru, yan sanda sun sanar cewa sun kama wasu da suke zargi suna cikin yan daba da suka kai hari majalisar su biyar.

Shi dai dan majalisar wanda ake nuna ma yatsa ya ziyarci zauren bayan zauren ta dakatar dashi na tsawon kwanaki 90 kan wata laifi da ta kama shi aikatawa wanda ya bijire ma ka'ida.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT