ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An sake kama Dino Melaye bayan ya tsere daga hannun jami'an tsaro

Yan sanda sun bi sahun sane har asibitin da aka kwantar dashi inda yake jinyar raunin da ya samu sakamakon durowa da yayi daga mota mai jigilar shi zuwa jihar Kogi

Yan sanda sun bi sahun sa ne har asibitin da aka kwantar dashi inda yake jinyar raunin da ya samu sakamakon durowa da yayi daga mota mai jigilar shi zuwa jihar Kogi.

A ranar talata 24 ga watan afrilu dan majalisar ya kufce daga jami'an tsaro yayin da suke kan hanyar gabatar dashi gaban babban kotu tarayya dake Lokaja nan jihar Kogi kan zargin da ake masa.

Sakamakon durowan da yayi a motar jami'an tsaro, sanata ya samu  rauni wanda bisa wannan dalilin aka garzaya dashi wata asibiti dake yankin Mabushi mai suna Zankli Medical Center.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan sanda Jimoh Moshood ya sanar, dan majalisar ya kufce daga hannun jami'an dake safarar shi tare da taimakon wasu yan tawaye magoya bayan shi.

ADVERTISEMENT

Kakakin ya kara da cewa za'a dauki mataki mai tsauri  kanshi domin gabatar dashi gaban kotu ba tare da bata lokaci idan ya murmure.

Kamar yadda labari yazo mana yan sanda sun mamaye asibitin da yake jinya kuma akwai yiuwar ya canza masa asibiti bisa dalilai na tsaro.

Zargin da ake yi ma Dino Melaye

Hargitsin  jami'an tsaro dasanatan ya fara ne tun ranar litinin a filin jirgin saman Abuja bayan da aka hana shi tafiya kasar waje.

Dan majalisar yaki amincewa da gayatar da jami'an tsaro suka yi masa don bada amsar zargin da ake masa.

ADVERTISEMENT

Ana zargin sa da daukar nauyin wasu yan tawaye da aka kama a jihar kogi masu haifar da rikicin siyasa a jihar.

Sai dai dan majalisar ya sha musanta wannan zargin inda ya danganci lamarin da aikin siyasa daga makiyin sa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT