ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An sace Amarya da yan rakiya su 10

Lamarin ya faru ne daren ranar asabar 31 ga watan Maris a karamar hukumar Birnin gwari dake jihar Kaduna

Lamarin ya faru ne yayin da ake kai amarya dakin mijinta  da misalin karfe 8:00 na daren ranar asabar 31 ga watan Maris wanda ya jefa al’ummar yankin cikin taraddadi da rashin tabbas.

Yayin da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, wani tsohon Shugaban karamar hukuma wanda ya bukaci a boye, masu garkuwar sun dakatar da motar wacce ke dauke da amaryar, inda suka yi awon gaba da ita da kuma ‘yan rakiyar ta su goma.

Ya ce, lamarin ya auku a tsakanin kilomita 55 daga garin Birnin Gwari. Sai dai rahotanni sun ce, uku daga cikin wadanda aka yi garkuwar dasu sun samu damar kubuta, inda suka dawo garin a jiya da safe.Sai dai kakakin hukumar yan sanda ta jihar Kaduna ya sanar cewa labarin bai isa gare su ba.

Birnin gwari yana daya daga cikin garuruwa dake fuskantar barazana da hare-haren yan fashi da masu garkuwa da mutane kuma al' amarin yaki ci kuma yaki cinyewa.

ADVERTISEMENT

Al'umma dai suna ta koke-koken kan a kawo masu dauki kan tarzomar da suke fuskanta a hannun yan ta'dda.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT