Pulse.ng logo
Go

Fadar shugaban kasa An nada sabon shugaban hukumar DSS wanda zai maye gurbin Lawal Daura

An nada shi ne bayan lamarin da ya faru a zauren majalisar dokoki wanda yayi sanadin sallamar Lawal Daura

  • Published: , Refreshed:
6 things you should know about the new DSS boss, Mathew Seiyefa play

Mathew Seiyefa - New DSS DG

(Lailas News)

Hukumar jami'an fararen hula ta DSS ta samu sabon jagora bayan am sallami tsohon shugaban ta Lawal Daura sakamakon lamarin da ya faru a harabar majalisar dokoki.

Dan jihar Bayelsa Mathew Seiyefa shine wanda ya maye kujerar korarren tsohon shugaban kasancewa shine jami'i mai matsayi mafi girma a hukumar.

Tsohon shugaban ya fuskanci sallama ne sakamakon kawanya da wasu jami'an rundunar DSS suka yi ma zauren majalisar tarayya inda suka hana shiga da fita.

Jim kadan bayan faruwar lamarin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sanar da matakin sallamar shugaban rundunar.

A rahoton da tashar telibijin na Channels tv ta fitar, shugaban kasa mai riko ya kuma gana da sabon shugaban hukumar tare da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement