Pulse.ng logo
Go

Amina Muhammed Tsohuwar ministan Nijeriya ta samu sarautar "Sarauniya" a jamhoriyar Nijar

Jamhoriya ta karrama tsohuwar ministan shugaba Buhari da sarautar "Sarauniya"

  • Published:
Tsohuwar ministan muhalli na Nijeriya Amina Muhammed play

Tsohuwar ministan muhalli na Nijeriya Amina Muhammed

Tsohuwar ministan muhalli karkashin shugabancin shugaba Buhari kuma mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya, Amina Muhammed, ta samu sarautar "Sarauniya" a kasar jamhoriyar Nijar.

Jakadiyar Nijariya a majalisar dinkin duniya ta samu sarautar ne yayin da ta kai ziyarar aiki kasar kashen makon da ya shude.

Amina Muhammed ta samu sarautar "Sarauniya" kasar jamhoriyar Nijar play

Amina Muhammed ta samu sarautar "Sarauniya" kasar jamhoriyar Nijar

(Twitter/halimahima)

 

Da wannan sabon nadin da ta samu, tsohuwar ministan zata shiga daga cikin masu bada umarni game da shugabanci a kasar tare da bada shawara ko gudunmawa.

Minsitan ta kai ziyara kasar ne domin gudanar da wasu ayyuka ta musamman domin taimakawa al'ummar kasar musamman mata da yara kanana.

Ta hadu da shugaban kasar Jamhoriyar Nijar, Mahamadou Issoufou, da uwardakin sa tare da sauran ma'aikatan majlisar shugaban.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement