ADVERTISEMENT

Shugabancin Najeriya sun ce ʼƴan matan Chibok zasu yi bikin kirsimeti da iyayensu

Garba Shehu ya ce Maʼaikatun Tsaro na Asirce, suna shawarwari domin samun ʼƴancin sauran ʼƴan matan Chibok waɗanda ke hannun ʼƴan Boko Haram.

Ƴan matan Chibok waɗanda sun tsira daga Boko Haram, za su yi bikin kirsimeti da sabon shekara tare da iyayensu. Wannan sanarwa ya fito daga bakin Malam Garba Shehu, Babban Mataimakin Shugaban Ƙasa akan Labaru.

Shehu ya baza wannan sannarwa akan shafinsa na Facebook. Ya cê Maikata masu tsaron ƙasa a asirce, sun tafi da ʼƴan matan Chibok zuwa wajen iyayensu.

Ya ƙaryata wasu rahotannin da ake bazawa akan yanan-gizo, cêwa an ƙara samun ʼƴancin wasu ʼƴan matan Chibok daga hannun ʼƴan Boko Haram. Ana yada jita-jita cêwa an gano wasu ʼƴan mata a Birnin Yola, kuma ana tsamanin cêwa an sake tsirar da wasu ʼƴan mata. Amma Garba Shehu ya bayyana cêwa waɗanan mata su ne waɗanda aka karɓa daga hannun ʼƴan Boko Haram a cikin watan Oktoba.

Shehu ya bayyana cêwa a cikin asirce,  Maʼaikatun tsaro suna cikin tattaunawa akan samun ʼƴancin sauran ʼƴan mata wanda suke hannun ʼƴan Boko Haram har yanzu. Kaman yanda ya bayyana, Malam Garba ya cê Sashen Gwamnati mai Tsaro cikin asiri, suna fata cêwa zasu ci saʼa. Garba ya yi bayani haka:

ADVERTISEMENT

"Abokaninmu masu yada labari cêwa an ƙara sakin wasu ʼƴan matan Chibok, ba mu yi saʼa ba tukuna."

"Har yanzu, muna cikin shawara. Sashen Gwamnati mai Tsaro cikin asiri suna imani cêwa za mu yi saʼa."

"Yau, ʼƴan hukumar DSS sun isad da ʼƴan matan Chibok ashirin zuwa Birnin Yola, a Jihar Adamawa, domin yin bikin kirsimeti da iyayensu."

"Ba a ƙara tsirar da wasu ʼƴan mata ba. Amma da ikon Allah, za a ʼƴantar da su. Ina gaisuwa: Barkan ku da bikin kirsimeti, jamaʼa."

Hukumar Labarai na Najeriya (NAN) sun tuna da labarin ʼƴan mata 276 wanda ʼƴan Boko Haram suka sace a yayin da sun fashe ɗakunansu cikin makarantan Chibok a shekara na 2104.

ADVERTISEMENT

A cikin watan Oktoba, Gwamnati ta samu saʼa na ƴantar da su , bayan sun tsawanta wajen tattaunawa da waɗanda suka sace su. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi alƙawari na tabbatar da cêwa an karɓi sauran matan da aka sace.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

3 food items legal in Nigeria but banned abroad

3 food items legal in Nigeria but banned abroad

Top 10 African countries with the highest crime rates

Top 10 African countries with the highest crime rates

5 Nollywood historical films you should see on October 1

5 Nollywood historical films you should see on October 1

6 key figures who paved the way for Nigeria’s Independence in 1960

6 key figures who paved the way for Nigeria’s Independence in 1960

Top 10 African countries with the cheapest data prices from June to September

Top 10 African countries with the cheapest data prices from June to September

Venita, Soma and Angel get evicted from Big Brother Naija All Stars

Venita, Soma and Angel get evicted from Big Brother Naija All Stars

Here's why guinea fowls make great security guards

Here's why guinea fowls make great security guards

How Editi Effiong delivered a global hit with 'The Black Book' [Exclusive]

How Editi Effiong delivered a global hit with 'The Black Book' [Exclusive]

The World Bank has warned that Nigeria may bear some of the brunt of the Niger coup

The World Bank has warned that Nigeria may bear some of the brunt of the Niger coup

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT