Pulse.ng logo
Go

A garin Abuja An kama yan shi'a 115 sakamakon arangama da suka yi da yan sanda

Rundunar tayi watsi da jita-jita dake yaduwa a kafafen sada zumunta mai cewa sakamakon hargitsin an rasa rayuka

  • Published:
‘Like Buhari, El-zakzaky deserves oversea medical treatment,’ says Shiites play

‘Like Buhari, El-zakzaky deserves oversea medical treatment,’ says Shiites

(Pulse)

Rundunar yan sanda na babban birnin tarayya ta sanar cewa ta kama wasu mabiyan darikar shi'a su dari da sha biyar sakamakon arangama da suka yi jiha a daidai Unity fountain dake yankin Maitama.

Rundunar tayi watsi da jita-jita dake yaduwa a kafafen sada zumunta mai cewa sakamakon hargitsin an rasa rayuka.

A wata takardar sanarwa da kakakin rundunar DSP  Anjuguri Manzah ya fitar, ya bayyana cewa ba'a rasa rai sakamakom tarzoman da ya faru domin jami'an sun nuna kwarewarsu wajen shawo kan rikicin.

Sai dai ya kara da cewa jami'a 22 suka jikkata sakamakon hargitsin kuma an gano wasu kanan makamai tare da wadanda suka kama.

Ya kara da cewa masu zanga-zangar sun barnatar da dukiyoyin jama'a a yankin kuma sun far ma al'umma tare da tayar da hankulan jama'a.

Police cracks down on Shiites protester demanding El-Zakzaky's release play

Protesters attacked by police in Abuja

(Twitter/@GbemiDennis)

Daga karshen kakakin ya kara da cewa, rundunar tare da hadin gwiwar jami'ai na musamman daga ofishin sifeton yan sanda na kasa zasu gudanar da bincike kan lamarin kana za'a gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu domin sauraron kara.

Yan shi'a sun gudnar da gangami ne domin nuna bacin ran kan tsaran jagoran su wanda aka garkame duk da damar da kotu ta bayar.

Tun ba yau ba suke gudanar da zanga-zanga cikin lumana kan lamarin sai dai lamarin na jiya ya keta haddi inda abun ya koma tamkar fito-na-fito tsakanin yan sanda da mabiyan akidar shi'a.

Gwamnati da El-zakzaky

A cikin shekara 2016 mai shari'a Gabriel Kolawole ya bada dama na a sake shi bayan gwamnati ta cigaba da tsaran shi kan dalilin kare lafiyar shi.

Mabiyan darikar shia sun kai koken su offishin HRC dake Abuja play

Mabiyan darikar shia sun kai koken su offishin HRC dake Abuja

 

Shekara biyu kenan da kai hari jagoran mabiya akidar shi'a na nijeriya a gidan sa dake Zaria wanda yayi sanadiyar kashe yaran sa uku da dinbim mabiyan sa. Bayan harin da sojoji suka kai mai sun kuma kama shi wanda har yanzu ana tsaran shi duk damar da kotu ta bayar.

Sojojin sun dirar masu ne sakamakon fito-mu-gama da ya faru tsakanin yan shi'a da tawagar hafsan sojojin Nijeriya janar Tukur Buratai, hanyar shi na barin Zaria yayin da yan shi'a ke gudanar da taron su wanda ya sanya har suka toshe hanya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.