Pulse.ng logo
Go

Siyasa An kai hari ofishin yakin neman zabe na Atiku dake jihar Katsina

maharan sun kai harin ne a daidai karfe 8:00 na daren ranar asabar 7 ga wata kuma sakamakon harin sun faffasa gilasan motoci da sauran sassa na motocin dake ajiye a harabar ofishin

  • Published:
Ex-VP, Atiku Abubakar praises withdrawal of policemen from VIPs play

Nigeria's former VP, Atiku Abubakar has watched Black Panther saying it's a good movie.

Mahara sun kai hari ofishin yakin neman zabe na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar dake unguwar dandagoro na karamar hukumar Batagarawa ma  jihar Katsina.

Harin dai ya faru yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta'aziya jihar ga iyalen tsohon dan majalisar dattawa Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu kwanan baya.

A bisa labarin da jaridar Premium times tayi, maharan sun kai harin ne a daidai karfe 8:00 na daren ranar asabar 7 ga wata kuma sakamakon harin sun faffasa gilasan motoci da sauran sassa na motocin dake ajiye a harabar ofishin.

Thugs attack Atiku's presidential campaign office in Buhari's Katsina play

Vehicle vandalised during an attack Atiku Abubakar's presidential campaign office in Katsina

(Premium Times)

 

Kamar yadda mai kula da ofishin mai suna Masa'udu Abdulkadir ya sanar,  babu wanda ya jikkata sakamakon harin da aka kai. Yace ana gyara ne a harabar sanda maharan suka kai harin.

Ya kuma kara da cewa, wannan lamarin ba zai hana yan goyon bayan Atiku cigaba da nuna goyon bayan su bisa kudirin sa na karawa da shugaba Buhari a zaben kasa da zai gudana a shekara mai zuwa.

A wata sanrwa da ya fitar, kakakin rundunar yan sanda na jihar Gambo Isah ya sanar cewa hukumar ta kama wasu da ake zargin suna cikin wadanda suka kai harin su uku kuma nan bada dadewa ba za; a gurfanar dasu gaban kotu.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.