Pulse.ng logo
Go

Jamhoriyar nijar An hana yan agajin kungiyar izala sanya unifom a Maradi

Ba tare da haufi, kungiyar tayi ammana da umurni inda har ga zuwa yanzu tana sa ran cewa za'a sanar da dalilin yin haka

  • Published:
An hana yan agajin kungiyar izala sanya unifom play

An hana yan agajin kungiyar izala sanya unifom

(jibwisrivers.com)

Yan sanda sun hana yan agajin kungiyar jama'atu izalatu bidi'a wa ikkamatus sunnah reshin jihar Maradi dake jamhoriyar nijar sanya rigar unifom na kungiyar.

A labarin da BBC ta fitar, shugaban yan agajin na garin ya shaida cewa umarnin ya fito a wata sako da jami'an tsaro suka tura mata.

Sai dai ba'a sanar da dalilin dakatar da sanya rigar bai daya na yan agajin. Shugaban ySulaiman Hashimu yana mai cewa "Jami'an tsaro na 'yan sanda ne suka bayar da umarnin. Mun tambaye su dalilin hakan sun ce su ma ba su san dalili ba umarni aka ba su daga sama,".

Ba tare da haufi, kungiyar tayi ammana da umurni inda har ga zuwa yanzu tana sa ran cewa za'a sanar da dalilin yin haka.

"Idan kuma aka dauki lokaci ba a gaya mana dalili ba to ba wani abu da za mu iya yi da kanmu dole sai abun da uwar kungiya ta kasa ta ce, don da umarninta za mu yi amfani," ya kara.

Jami'am gwamnatin jihar basu yi karin haske kan lamarin ba sai dai, sun sanar cewa zasu tuntubi manema labarai nan bada jimawa ba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.